A shekarar 2007, yayin da Rwanda ta shiga kungiyar gamayyar tattalin arzikin kasashen gabashin Afirka, ta daina matsayinta a kungiyar gamayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka. Game da wannan batu, gwamnatin kasar Ruwanda ta bayyana cewa, kasar ta yi haka ne domin kauracewa tsayawa cikin kungiyoyi biyu masu manufa iri daya.
A cikin 'yan shekarun da suka wuce, hadin gwiwa tsakanin Rwanda da Congo Brazzaville da Gabon da sauran kasashen tsakiyar Afirka ta kara karuwa, har ma an kafa hanyar zirga-zirgar jirgin sama tsakanin hedkwatocin wadannan kasashe uku. Louise Mushikiwabo ta bayyana cewa, bayan samun ci-gaban bunkasuwar tattalin arzikin kungiyar kasashen gabashin Afirka, mu'amala tsakanin Rwanda da kasashe membobin kungiyar gamayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka ta karu sosai. A sakamakon haka, a ganin Rwanda yanzu lokaci ya yi na sake komawa cikin wannan kungiya.(Fatima)