in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na Ruwanda
2012-05-22 20:14:35 cri
Yau 22 ga wata a nan birnin Beijing, ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi ya gana da takwararsa ta kasar Ruwanda Louise Mushikiwabo wadda ke yin ziyara a kasar Sin.

A yayin ganawar, Yang Jiechi ya ce, a sabon yanayin da ake ciki, bangaren Sin yana son hada kai da bangaren Ruwanda a kokarin daga dangantakar hadin gwiwa irin ta sada zumunta a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. Sannan Mr. Yang ya gayyaci minista Louise Mushikiwabo na kasar Ruwanda da ta halarci taron ministoci karo na biyar na dandalin tattaunawar hada kan kasashen Sin da Afirka da za a shirya a watan Yuli mai zuwa a nan Beijing. Mr. Yang ya kara da cewa, bangaren Sin da dukkan mambobin dandalin, ciki har da kasar Ruwanda za su kara tattaunawa kan yadda za su iya samun wasu sabbin hanyoyi da daukar sabbin matakai a kokarin zurfafa dangantakar abokantaka irin ta sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Afirka, ta yadda za a iya ciyar da sabuwar huldar abokantaka dake kasancewa tsakanin Sin da kasashen Afirka gaba a kai a kai.

A nata bangaren, madam Louise Mushikiwabo ta yaba da sakamakon a zo a gani da kasashen Sin da Afirka suka samu a inuwar dandalin tattaunawa na hada kan kasashen Sin da Afirka. Ta bayyana cewa, bangaren Ruwanda zai halarci taron ministoci karo na biyar na dandalin, kuma zai hada kai da bangaren Sin kan yadda za a iya samun sabon ci gaba wajen bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Afirka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China