in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan kasar Sin ya gana da ministar harkokin wajen kasar Ruwanda
2012-05-23 20:38:42 cri
Ranar Laraba 23 ga wata, a nan Beijing, Hui Liangyu, mataimakin firaministan kasar Sin ya gana da madam Louise Mushikiwabo, ministar harkokin wajen kasar Ruwanda.

A yayin ganawar, mista Hui Liangyu ya ce, kasar Sin na son yin kokari tare da kasar ta Ruwanda wajen kara inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 da ma al'amuran kasa da kasa, a kokarin raya huldar abokantakar da ke tsakaninsu zuwa sabon mataki. Haka kuma, mista Hui ya nuna cewa, akwai kyakkyawan tushe wajen kara zurfafa hakikanin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Ruwanda. Ya kamata bangarorin 2 su yi hangen nesa da sabunta tunaninsu, tare da yin amfani da sassan da ba su taba amfani da su ba, domin sa kaimi kan samun sabon ci gaba ta fuskar yin hadin gwiwa a tsakaninsu.

A nata bangaren kuma, madam Mushikiwabo ta ce, har kullum Ruwanda da Sin suna bunkasa huldar abokantaka a tsakaninsu bisa tushen girmama juna. Kasarta ta gode wa kasar Sin sosai bisa ga goyon baya da taimakon da take bayarwa a fannin farfado da tattalin arziki da zaman al'ummar Ruwanda. Ruwanda za ta tsaya tsayin daka kan raya huldar da ke tsakaninta da Sin, kana kuma tana son kasancewa wata gada ce wajen inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin Sin da yankin gabashi da tsakiyar Afirka. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China