Shugaban tawagar Gao Zhongxian ya bayyana cewa, a halin yanzu, akwai likitoci guda hudu a asibitin garin Rulindo, shi ya sa, tawagar ba da agajin Sin ta ga da cewar horas da likitocin asibitin, wajen kyautata fasahohinsu, ta yadda za su iya ba da taimako ga karin marasa lafiya.
A wannan rana, jakadan Sin da ke kasar Rwanda ya halarci bikin, inda ya bayyana cewa, tun shekarar 1982, kasar Sin ta fara tura tawagogin ba da agajin kiwon lafiya zuwa kasar ta Rwanda, don samar da taimakon jinya ga jama'ar kasa, da kuma biyan bukatunsu.
A nasa bangare, shugaban jihar Arewa Aime Bosenibamwe ya nuna matukar godiya ga tawagogin ba da agajin kiwon lafiyar Sin, har ila yau, a madadin gwamnati da jama'ar kasa, ya bayyana fatan samun karin likitocin kasar Sin a kasar Rwanda. (Maryam)