A gun taron manema labaru da aka gudanar bayan ganawar tsakanin shugabannin biyu, shugaba Kagame ya bayyana cewa, shi da shugaba Bango sun yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar kasashen biyu da batutuwan yankin da suke sa lura tare. A ganinsu, kara inganta dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, musamman kara zuba jari da hadin gwiwa a tsakaninsu sun kasance muhimmin aiki yayin da ake kokarin inganta dangantakarsu.
Kagame ya nuna gamsuwa ga ci gaban dangantakar kasashen biyu a yanzu, kana ya ce zai sa kaimi ga kamfanoni masu zaman kansu na kasar Ruwanda da su fita waje, da neman damar zuba jari da hadin gwiwa a kasar Gabon. Ya ce, hukumar kula da harkokin zuba jari ta gwamnatin kasar Ruwanda tana kokarin taimakawa kamfanoni masu zaman kansu na kasar wajen samun damar zuba jari a kasar Gabon, domin za a samu babban ci gaba wajen zuba jari da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, tare da kawowa jama'ar kasashen biyu babbar moriya.
A gun taron manema labaru, shugaba Bango ya bayyana cewa, burin ziyararsa a kasar Ruwanda shi ne neman damar zuba jari da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. Ya ce, a halin yanzu, kasar Gaban tana dogaro da kudin da ake samu daga man fetur. Kara zuba jari da hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen dake dab da ita kamar kasar Ruwanda shi ne babban mataki na kasar Gabon wajen samun bunkasuwar tattalin arziki ta hanyoyi daban daban. (Zainab)