in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya aike da wasikar gaisuwa ga ma'aikata masu ba da jinyar cutar kanjamau
2013-12-01 17:16:01 cri

Yau Lahadi 1 ga watan Diasamba, ranar yaki da cutar kanjamau ta kasa da kasa ce, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya aike da wata wasika zuwa asibitin You'an dake birnin Beijing, inda ya yi gaisuwa da kuma nuna matukar godiya ga dukkan likitoci, ma'aikatan da abin ya shafa, kungiyoyin zaman takewar al'umma da kuma masu aikin sa kai wadanda suke dukufa wajen gudanar da ayyukan yaki da cutar kanjamau, ya kuma kara kwarin gwiwa ga wadanda suka kamu da cutar.

Bugu da kari, a madadin firaminista Li Keqiang, yau ranar 1 ga watan Disamba, mataimakiyar firaministan kasar Sin, shugabar kwamitin kula da harkokin yakin da cutar kanjamau na majalisar gudanarwa ta kasar Liu Yandong ta kai ziyarar aiki a asibitin You'an don mika wasikar firaminista Li Keqiang, da kuma duba ayyukan yaki da cutar kanjamau na wannan asibiti da kuma yin ganawa da masu fama da cutar.

Cikin wasikar, Mr. Li ya bayyana cewa, saurin karuwar adadin masu fama da cutar kanjamau na kasar Sin ya ragu sosai bisa kokarin gwamnati da kuma masu aikin yaki da cutar kanjamau na kasar cikin shekaru da dama da suka wuce, wannan na da muhimmanci ga kasar Sin wadda ke kunshi da mutane masu dimbin yawa, kuma babbar kasa ce mai tasowa. Kuma yana fata za a ci gaba da dukufa kan wannan aiki a nan gaba, tare da ba da kulawa ga masu fama da cutar yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China