Hukumar yaki da cutar Sida ta MDD a ranar Laraban nan 20 ga wata ta ce, za ta kara daura damarar yaki da cutar a kudancin Turai, tsakiyar Asiya, yankin Gabas ta Tsakiya, arewacin Afrika da kuma wassu wurare masu yawan al'umma.
A cikin wani rahoton da aka gabatar gabannin zuwan ranar cutar Sida ta duniya, hukumar ta ce, ana ta samun wadanda suka kamu da cutar da dama yanzu a kudancin Turai, tsakiyar Asiya, kuma hakan yana karuwa a kullum yanzu ya kai kashi 13 a cikin 100 tun daga shekara ta 2006, sannan kuma a yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika, wannan adadin ya ninka sau biyu tun daga shekara ta 2001.
Bayanin ya yi nuni da cewar, a wadannan wurare da ake samun karuwar mazaje dake saduwa da mazaje, masu shan miyagun kwayoyi, masu canja jinsi, masu sana'ar karuwanci, ana hana su damar samun taimakon magani don inganta lafiyarsu.
Rahoton da aka gabatar ya gano cewar, tallafin da ake bayar wa musamman domin mazaje dake saduwa da mazajen masu dauke da cutar a yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika, da ma sauran kasashen Afirkan dake kudu da hamadar Sahara ba ya kai wa ga wadanda ake bukata.
Hukumar ta yi kira da a kara mai da hankali a kan yara da manya da suka haura shekaru 50 dake fama da wannan cuta, yana mai bayanin cewar, magungunan wannan cuta ta Sida na yara kashi 34 ne a cikin 100 wadanda har yanzu ke a matsayin rabin wanda ake ba manya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, yanzu haka yawan manya dake fama da wannan cutar wadanda suka haura shekaru 50 yana karuwa, abin da ke neman ya zama ruwan dare. (Fatimah)