Babban taken ranar yaki da cutar kanjamau ta shekarar 2012 shi ne 'tabbatar da samun sifiri, wato babu wanda ya fara kamuwa da cutar kanjamau, babu mutanen da suka mutu sakamakon cutar, kuma babu nuna bambanci.' Ta la'akari da yadda cutar take bazuwa a duniya, za a ga zai yi wuya sosai wajen cimma burin 'tabbatar da samun sifiri', amma kasashen duniya na kokarin samun ci gaba a wannan fanni.
A babban taron MDD da ya gudana a shekarar 2011, gwamnatocin kasashe daban daban sun yarda da sanya buri na 'baiwa masu dauke da cutar kanjamau miliyan 15 na duniya maganin da zai ceto rayukansu a shekarar 2015'. Game da batun, jami'an hukumar WHO sun ce, bisa kididdigar da aka yi, an yi hasashen cewa, idan kasashe daban daban za su iya ci gaba da kokarin da suke a halin yanzu, to, za a iya cimma burin da aka sanya gaba. (Bello Wang)