Madam Bokova ta ce, har yanzu dai cutar kanjamau na daya daga cikin cuttuttukan da suka fi kawo illa ga rayuwar al'umma a duniya. Dole ne a kara zage damtse domin cimma burin "kawar da sabbin masu dauke da kwayoyin cutar, rashin nuna musu wariya ko bambanci, da kuma kawar da wadanda ke mutuwa sanadiyar cutar". Kamata ya yi a kyautata tsarin yaki da cutar, da daukar sabbin matakai domin hana mutane kamuwa da cutar, kana da magance mutuwar mutane sakamakon cututtukan da ke da nasaba da cutar.
Ta kuma jaddada cewa, domin cimma wannan buri, kungiyar UNESCO za ta goyi bayan kasa da kasa wajen kyautata aikin koyar da matasa hanyoyin kamuwa da cutar kanjamau da kuma jima'i, da mara wa ma'aikatun ilmi na kasa da kasa baya wajen hada kai tare da ma'aikatunsu na kiwon lafiya, a kokarin ba da tabbaci ga matasa wajen samun ilmi da fasaha da ake bukata don lafiyar jiki. Bugu da kari kuma, mata da yara rukunoni ne da cutar kanjamau ke yiwa illa, wadanda suka zama muhimmin sashe a cikin ayyukan yaki da cutar.
Bisa kididdigar da kungiyar UNESCO ta bayar, an ce, yawan baligai da yara da suka kamu da cutar kanjamau a shekara ta 2011 ya ragu da kashi 20 cikin dari bisa na shekara ta 2001. Haka kuma daga shekara ta 2005 zuwa ta 2011, yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya ragu da kashi 32 cikin dari a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara. Amma ya zuwa karshen shekara ta 2011, ana iya samun mutane miliyan 34 da ke fama da cutar a duk duniya.(Kande Gao)