in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 30 sun mutu sakamakon faduwar wani jirgin saman fasinja a Kongo Kinshasa
2013-03-05 10:03:00 cri

Wani jirgin saman fasinja ya fadi a gabashin kasar Kongo Kinshasa a ran 4 ga wata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 30.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan jirgin sama samfurin "Fokker 50" mallakar wani kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar ne mai suna CAA. An kuma ba da labarin cewa, wannan jirgin na dauke ne fasinjoji 40, ya kuma tashi daga birnin Lodja dake tsakiyar kasar zuwa birnin Gome dake gabashin kasar.

Jirgin dai ya fadi ne a tsakiyar birnin Gome sakamakon ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya ke, yayin da ya yi kokarin sauka.

Wani kamfanin dillancin labaru na Afirka ta kudu ya ruwaito shugaban birnin Gome cewa, an riga an gano mutane 4 wadanda suka tsira da ransu, kuma faduwar jirgin ba ta jawo hasarar rayuka da raunata jama'a dake kasa ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China