A matsayin aiki daya bayan taron tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, taron tattaunawa a tsakanin magadan biranen Sin da na kasashen Afirka ya kasance wani muhimmin aiki wajen raya sabuwar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu.
Tsohon shugaban kwamitin kungiyar AU Jean Ping ya halarci bikin bude taron tattaunawar, kana kungiyar kula da harkokin sada zumunta a tsakanin jama'ar Sin da ta kasashen waje ta ba shi lambar yabo ta manzon sada zumunta na jama'a. A cikin jawabinsa, Jean Ping ya nuna cewa, tsarin samun bunkasuwa na kasar Sin abin al'ajabi ne, kuma kasashen Afirka suna son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a dukkan fannoni. (Zainab)