in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na samun damar kara kyautatuwa
2013-06-18 18:02:52 cri
A yau 18 ga wata, Mr. Liu Guijin, tsohon wakilin farko na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka, kuma shugaban kwalejin cinikayya na Sin da Afirka na jami'ar horar da malamai ta Zhejiang ya bayyana cewa, yanzu hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na samun damar kara kyautatuwa, ta yadda za a kara yin moriyar juna tsakaninsu. Sabili da haka, ana bukatar karin kwararru a fannoni daban daban.

A yayin taron tattaunawa kan batun shigar da 'yan kasuwa na Zhejiang a kasashen Afirka da aka shirya a lardin Zhejiang, Mr. Liu Guijin ya ce, kasashen Sin da Afirka suna da makoma mai haske sosai wajen yin hadin gwiwa irin ta moriyar juna.

Sannan Liu Guijin ya nuna cewa, idan ana son kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya domin tabbatar da samun ci gaba ba tare da tangarda ba, ya kamata a sa kaimi ga bangarori biyu da su canja salon yin hadin gwiwa, a kokarin yin gyare-gyare kan salon yin hadin gwiwa domin kara kyautata shi, da ingancinsa, ta yadda irin wannan hadin gwiwa za ta kai wani sabon matsayi.

Bugu da kari, Liu Guijin ya jaddada cewa, ana bukatar karin kwararru wadanda suke da ilmomi iri daban daban. Sabo da haka, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su yi kokarin yin hadin gwiwa a fannin ilmantarwa, ta yadda za a iya horar da karin mutane wadanda za su iya ci gaba da bunkasa hadin gwiwar irin ta sada zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China