A wannan rana kuma, kwamitin kula da harkokin diplomasiyya na majalisar wakilan kasar Amurka ya kira wani taron sauraren ra'ayin jama'a kan batun daukar matakan soja a kasar Syria. Yayin taron, sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya bayyana cewa, matakan sojan da Amurka za ta dauka za su iya rage karfin sojan gwamnatin kasar Syria, in ba haka ba, kila gwamnatin Bashar al-Assad za ta ci gaba da yin amfani da makamai masu guba a kasar.
Ran 4 ga wata, shugaban hukumar tarayyar kasashen Turai Von Rompuy ya bayyana cewa, batun yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria ya saba wa dokokin duniya, shi ya sa ya kamata gamayyar kasa da kasa ta hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.
A wannan rana kuma, an shafe kusan sa'o'i biyu ana tattauna kan batun ko za a dauki matakan soja kan kasar Syria ko a'a a majalisar dokokin kasar Faransa, amma ba a jefa kuri'a kan batun ba a yayin tattaunawar. Kana bisa labaran da aka samu daga kafofin watsa labaran kasar Faransa, an ce, ba a tattauna kan batun ba cikin taron majalisar dokokin kasar, wakilan manyan jam'iyyu ne kawai suka bayyana ra'ayoyinsu kan batun.
Ran 4 ga wata, kan halin da kasar ke cikin yanzu, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal al-Mekdad ya bayyana cewa, idan kasashen Isra'ila, Turkiya da kuma Jordan za su dauki matakan soja kan kasar, kasar Syria za ta mayar da martani kan kasashen. Ya kuma kara da cewa, ko wane irin matakan soja da za a dauka kan kasar Syria zai haddasa tabarbarewar yanayi a duk fadin yankin.
Ran 4 ga wata, a birnin Teheran, shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya bayyana cewa, matakan soja da kila kasar Amurka za ta dauka kan kasar Syria ba za su dace da moriyar ko wane bangare ba, ya kuma jadadda cewa, ya kamata a tsara makomar kasar Syria bisa bukatun jama'ar kasar kuma ta hanyar jefa kuri'a a kasar. (Maryam)