A sa'i daya kuma ya jadadda cewa, ya kamata a nemi iznin kwamitin sulhu na MDD kafin a dauki ko wane irin matakin soja kan zargin yin amfani da makamai masu guba da akewa mahukuntan kasar.
Don gane da wannan batu shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a yau din nan cewa, ya kamata a nemi iznin kwamitin sulhu na MDD, kafin a dauki matakan soja a Syria, yana mai cewa, ko wane irin matakin soja da za a dauka kan Syria ba tare da iznin MDD, na iya zama yakin da ba shi da goyon bayan doka wato hari ne. (Maryam)