A jiyan ne kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gayyaci shugabannin majalisar dokokin kasa don su halarci wani taro a fadar shugaban kasa ta White House, inda ya nemi goyon bayan su kan batun daukar matakan soja a Syria. Bayan wannan taron kuma, shugaban majalisar wakilan kasar John Boehner da kuma shugaban masu rinjiye na jam'iyyar Democratic Party a majalisar walikan kasar Nancy Pelosi dukkansu sun nuna goyon baya ga shugaba Barack Obama wajen daukar matakan soja kan kasar Syria. A wannan rana kuma, kwamitin kula da harkokin diplomasiyya na majalisar dattawar kasar Amurka ya fidda wani daftari game da batun daukar matakan soja kan kasar Syria, inda ya tsaida wa'adin kwanaki 60 wajen daukar matakan soja kan kasar Syria, kuma idan za a iya gabatar wa majalisar dokokin kasar bayanai kafin lokaci, za a iya tsawaita aikace-aikacen matakan soja zuwa kwanaki 30, watau kwanaki 90 ke nan a jimilce.
Ran 3 ga wata, kakakin babban wakilin kula da harkokin tsaro da na diplomasiyya na kungiyar tarayyar kasashen Turai Michael Mann ya bayyana cewa, ya kamata a dauki matakai bayan tawagar bincike ta MDD ta gabatar da rahotonta game da batun kai hari ta hanyar yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria. (Maryam)