Kasancewar hare-haren sun auku ne a ranar bikin Karamar Sallah, lokacin da jama'a da dama ke gudanar da bukukuwa, hare-haren sun haddasa rasa rayuka da raunatar mutane da dama.
Tun farkon wannan shekarar ta bana, ake ta samun hare-haren ta'addanci a kasar Iraki, wadanda suka kawo babbar illa ga zaman lafiya a kasar. Bisa kididdigar da tawagar MDD dake kasar Iraki ta yi a kwanakin baya, an ce, a sakamakon hare-haren da aka kai wa kasar Iraki a watan Yulin bana, mutane 1057 ne suka mutu, baya ga wasu 2326 da suka ji raunuka, don haka wannan wata ya kasance watan da aka fi samun mutuwa da raunatar mutane a cikin shekaru 5 da suka gabata. (Zainab)