A ran 1 ga wata a birnin Tehran, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Iran Ramin Mehmanparast ya ce, shigar da kasar Falesdinu cikin kungiyar UNESCO ta nuna cewa al'ummomin kasa da kasa sun nuna goyon gaya ga kasar Falesdinu. Ya ce, bai kamata kasar Amurka ta sa karfen kafa a duniya ba, ya kamata ta fahinci halin da ake ciki kan batun Falesdinu. Kuma ya bukaci kasar Amurka da ta dakatar da nuna goyon baya ga kasar Isra'ila daga dukkan fannoni, Yana ganin cewa, wannan matakin da kasar Amurka ta dauka zai bata sunanta a idon duniya. (Zainab Zhu)