Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya furta a ranar Laraba a birnin Accra cewa, makomar tattalin arzikin kasarsa na da kyau, duk da cewa za'a fuskanci kalubaloli na wucin gadi.
Tattalin arziki na amsawa cikin armashi domin matakan da aka dauka na jurewa wasu matsaloli, in ji shugaban kasar.
Mista Mahama ya yi wadannan kalamai a yayin bude bikin baje kolin kasa karo na hudu a Accra bisa taken dangantaka da kirkirowa domin cigaba.
'Mun nuna fargaba a baya bayan nan kan ingancin bashi. Mizalin cin bashin mu bisa la'akari da GDP, an kayasta shi a kan kashi 49.3 cikin 100. Ana cikin babbar bukatar cin bashi domin biyan bukatun da ake da su kan cigaban abubuwan more rayuwar jama'a, amma duk da haka, ina tabbatar muku cewa, za'a daidaita karfinmu na cin bashi gwargwadon yadda ya dace.' in ji shugaba Mahama.
Babban taron siyasar kasa, an shirya shi a karon farko a shekarar 2010, inda aka samu mahalarta fiye da 70 daga ofishin ministocin kasar, ma'aikatu da hukumomin gwamnatin, har ma da na majalisu, kananan hukumomin yankunan kasar baki daya. (Maman ADA)