in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran da hukumar IAEA sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa
2013-11-12 15:24:38 cri
A ranar Litinin 11 ga wata, a birnin Tehran hedkwatar kasar Iran ne, shugaban kungiyar kula da harkokin makamashi ta kasar Iran Salihi da shugaban hukumar makamashi ta duniya IAEA wato Yukiya Amano suka rattaba hannu game da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu, inda suka amince da masu bincike na hukumar IAEA su bincike wasu na'urorin nukiliya na kasar Iran.

Bisa yarjejeniyar da aka daddale, an ce, Iran ta amince da ma'aikatan hukumar IAEA su binciki muhimman tashoshi biyu na nukuliyar kasar, amma yarjejeniyar, ba ta shafi sansanin soji na Parchin ba.

Salihi ya ce, daddale yarjejeniya ya nuna cewa, Iran tana fatan taimakawa hukumar IAEA da kawar da shakkun da ake nuna wa Iran, da mayar da martini ga wadanda ke fafutukar kawo cikas na ganin batun nukiliya na kasar Iran ya samu ci gaba.

A wannan rana kuma, Iran da Birtaniya sun tura wa juna mukadashin mazannin, don fara yin mu'amalar diplomasiyya, bayan da aka katse dangantakar diplomasiyya cikin shekaru 2 da suka gabata. Gwamnatin Iran ta nada Mohammad-Hassan Habibollahzadeh don ya zama manzon kasar Iran a Birtaniya, yayin da kasar Birtaniya ma, ta tura Ajay Sharma don ya zama manzonta a kasar Iran.

Amma, a ranar 11 ga wata, a birnin Abu Dhabi, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Forbes Kerry ya bayyana cewa, Iran ba ta amince da shawarwarin da kasashe 6 da batun nukiliya na kasar ta Iran ya shafa ba, haka kuma, Amurka za ta ci gaba da kakabawa Iran takunkumi. Ya ce, idan Iran ta mallaka nukliliya, zai kawo barazana ga yankin baki daya, ciki har da kasar Isra'ila, don haka Amurka za ta ci gaba da sanya mata takunkumi, har zuwa lokacin da aka cimma matsaya guda da za ta gamsar sauran sassan da abin ya shafa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China