Madam Catherine Ashton, babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiya da tsaro ce ta wakilci kungiyar a taron, yayin da ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohanmed Javad Zarif ya wakilci tawagar kasar ta Iran, baya ga wakilan kasashen Burtaniya, Sin Faransa, Rasha, Amurka da kuma kasar Jamus.
Ana saran yayin taron na kwanaki biyu, kasashen da batun nukiliyar kasar ta Iran ya shafa, za su yi kokarin bullo da matakin farko da kasar Iran na warware matsalar nukiliyar kasar, ko da yake dukkan sassan sun bayyana yiwuwar cimma matsaya.
A tattaunawar da ta gabata wadda aka gudanar daga ranar 15-16 ga watan Oktoba, kasar Iran ta gabatar da wani shiri a matsayin wani mataki na sasantawa, amma ba a yi wani karin bayani game da shirin ba. (Ibarhim)