in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga bangarori da abin ya shafa da su yi shawarwari don dadaita matsalar nukiliya ta Iran tun da wuri
2013-11-10 16:44:31 cri

A ran 10 ga wata da alfijir bisa agogon wurin a Geneva, aka kammala shawarwari na sabon zagaye da kasashe shida wato Amurka, da Britaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin da Jamus suka yi da kasar Iran kan matsalar nukiliya ta Iran, wadanda aka shafe kwanaki uku ana yinsa. Ko da yake bangarorin da suka halarci shawarwari sun tattauna cikin yakini, amma ba su samu cimma tudun dafawa ba kamar yadda aka yi fata. Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Mista Li Baodong da ya halarci shawarwarin ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga bangarori da abin ya shafa da su ci gaba da yin shawarwari, domin dadaita matsalar nukiliya ta kasar Iran tun da wuri.

Bayan shawarwarin, Mista Li ya gaya wa manema labarai cewa, bangarorin suna son ci gaba da tattaunawa, da kuma kaddamar da shawarwari karo na gaba tun da wuri, bugu da kari kuma, suna son samun dabara a karshe domin daidaita matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar yin tattaunawa, da samu ra'ayi daya, da rage bambancin ra'ayi. Ya kara da cewa, har kullum kasar Sin tana nacewa wajen daidaita matsalar nukiliya ta Iran cikin lumana da diplomasiyya, sabo da haka Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga bangarori da abin ya shafa da su yi shawarwari don dadaita matsalar tun da wuri.

Za a ci gaba da shawarwarin a ranar 20 ga watan Nuwamba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China