Sin na fatan hukumar IAEA za ta karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Iran
A ranar Talata 29 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, Sin tana marhabin da mu'amala tsakanin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA da kasar Iran cikin yakini, kuma Sin ta sa kaimi ga hukumar IAEA da ta kara yin shawarwari da hadin gwiwa tsakaninta da Iran, ta yadda za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yin shawarwari tsakaninsu da daidaita batun nukiliya na Iran cikin lumana.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku