in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun nukiliya na Iran wata matsala ce mai jirkitawa, ba za a iya daidaita ta cikin sauri ba
2013-11-11 20:25:25 cri

A 'yan kwanakin baya, kasashe shida suka kammala shawarwarin da suka yi da Iran kan batun nukiliya na kasar. Da yake amsa tambayoyin manema labaru dangane da haka, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mista Qin Gang ya bayyana a ranar Litinin 11 ga wata a birnin Beijing cewa, batun nukiliyar kasar Iran wata matsala ce mai jirkitarwa, kasashe shida sun shafe shekaru goma suna yin shawarwari da kasar Iran, abin da ya nuna cewa wannan batu ba za a iya warware shi cikin sauri ba. Ya yi bayanin cewa, har kullum kasar Sin tsaye take kan ganin an daidaita matsalar ta hanyar tattaunawa da yin shawarwari, kuma kasar Sin tana rike da matsayinta na adalci, cikin yakini wanda ya sa take lallashin bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi shawarwari da juna. Kasar Sin in ji shi, za ta ci gaba da yin cudanya da bangarorin da abin ya shafa, a kokarin daidaita matsalar ta hanyoyin siyasa da diplomasiyya sannan kuma a cikin lumana.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China