in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan za a samu ci gaba kan shawarwarin batun nukiliyar kasar Iran
2013-11-07 20:15:14 cri
Ran Alhamis 7 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata bangarori daban daban da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa su dauki matakai yadda ya kamata don warware matsalar nukiliyar kasar, kuma Sin na fatan za a samu ci gaba mai ma'ana kan shawarwarin batun cikin sauri.

A ran Laraba 6 ga wata ne, wani jami'in Amurka ya bayyana cewa, Amurka za ta ba da shawara kan hanyar kawar da takunkumin da aka kakaba wa kasar Iran, amma ba zai shafi muhimmin bangare na takunkumin ba.

Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako da kuma yin hadin gwiwa da bangarorin daban daban da abin ya shafa kan yadda za a warware batun nukiliyar kasar ta Iran, kuma tana fatan za a samu sakamako mai gamsarwa yayin taron Geneva karo na biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China