Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Marzih Afkham, ya tabbatar a ranar 8 ga wata cewa, Iran ta riga ta kafa dangantakar diplomasiiya bias matsayin wakilin ofishin jakada a tsakaninta da kasar Britaniya.
Afkham ya gayawa kafofin watsa labarai cewa, a ran 7 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Britaniya William Hague ta tattauna da takwaransa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif ta wayar tarho, inda ya gabatar masa da shawarar aika wa juna mukaddashin wakilin jakada na wucin-gadi, zuwa manyan biranan kasashen 2. Kuma bangarorin biyu sun riga sun cimma matsaya daya kan wannan batu a ranar 8 ga wata.
Afkham ya ce, dama a baya jami'an kasashen Biyu sun taba tattaunawa kan yiwuwar daukar wannan mataki, yayin babban taro MDD da aka yi a watan da ya wuce a birnin New York. Bayan da aka kafa dangantaka bisa wannan matsayi, jami'an bangarorin biyu kuma za su iya musanyar ra'ayoyi kan dangantakar dake tsakaninsu, ciki hadda matsalar nukiliyar kasar Iran, da halin da shiyyar gabas ta tsakiya ke ciki da dai sauransu.
Idan dai za a iya tunawa a watan Nuwambar shekara ta 2011 ne dubban dalibai da jama'ar Iran suka rushe ofishin jakadancin Britaniya da ke birnin Teheran, babban birnin kasar Iran. A wani mataki na nuna adawa ga sabon takunkumin da Britaniya ta kakabawa Iran.
Wannan ne ya sanya Britaniyar a wancan lokaci, ta sanar da rufewa ofishin jakadancin nata dake Iran, kuma ta janye dukkan jami'an diplomasiyyar ta, tare da bukatar Iran din ta rufe ofishin jakadancin ta dake Britaniya ba tare da wani bata lokaci ba, ta kuma kwashe ma'aikatan diplomasiyyar ta daga Birtaniyan. Matakin da ya sanya tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen Biyu. (Danladi)