Ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Sin na fatan za a iya yin shawarwari yadda ya kamata bisa ka'idar girmamawa juna da kuma daukar matakan da za su dace don ciyar da harkokin shawarwari gaba, ta yadda za a iya samar da damar da ta dace dangane da warware matsalar nukiliyar kasar Iran yadda ya kamata, daga dukkan fannoni kuma cikin dogon lokaci.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu, an ce, za a gudanar da taron shawarwari kan batun nukiliyar kasar Iran na sabon zagaye a ranar 7 ga watan da muke ciki a birnin Geneva, kuma kasar Sin za ta aike da wata tawaga zuwa taron karkashin jagorancin shugaban sashen kula da harkokin kayyade makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Pang Sen. (Maryam Yang)