Hukumar kula da harkokin nukiliya ta MDD ta bayyana cewa, za a ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumar da kasar Iran a kwana na biyu ranar Talata 29 ga wata, game da shirin kasar na nukiliya da ake takaddama a kai.
Hukumar kula da makamashin nulkiya ta duniya IAEA ta bayyana cewa, ana sa ran shugaban hukumar Yukiya Amano zai bayar da sanarwa bayan tattaunawar ta ranar Talata tsakanin sassan biyu.
A ranar Litinin ne aka fara wannan tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, game da batun yadda za a nazarci muhimman takardu na cibiyoyin nukiliyar kasar, bayan ganawa tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da Mr. Amano.
A baya dai, hukumar ta IAEA ta yi ganawa sau 12 da Iran tun a shekara ta 2011, amma babu wani tudun dafawa da aka cimma game da duba cibiyoyi da baki dayan shirin nukiliyar kasar ta Iran. (Ibrahim)