Shugaba Xi ya yi wannan bayani ne a yayin da yake ganawa da Ali Larijani, shugaban majalisar dokokin kasar Iran da ke ziyara a kasar Sin a wannan rana. Ya kara da cewa, kasar Sin a tsaye take kan daidaita hulda a tsakaninta da Iran bisa manyan tsare-tsare da hangen nesa, tana son gama kai da Iran wajen ci gaba da inganta zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasashen 2, da kara azama kan bunkasuwar dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban yadda ya kamata.
A nasa bangaren kuma, Larijani ya ce, kasarsa ta Iran na dora muhimmanci kan raya hulda a tsakaninta da kasar Sin, tana sa ran inganta mu'amala da hadin gwiwa tare da Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, makamashi, zuba jari da dai sauransu. Kana kuma Larijani ya yi wa mista Xi bayani dangane da ra'ayin Iran kan batun nukiliyar da kuma halin da ake ciki a shiyya-shiyya.(Tasallah)