in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla sai bayan shekara daya ya kamata kafin Iran ta fara sarrafa makaman nukiliya, in ji Obama
2013-10-06 17:01:47 cri
Ran 5 ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, kasar Iran na bukatar shekara guda ko karin lokuta wajen sarrafa makaman nukiliya a kasar. Kuma wannan shi ne bayanin da hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta bayar, bayan nazarin da ta yi.

Amma bisa nazarin da kasar Isra'ila ta yi, an ce, kasar Iran za ta iya sarrafa makaman nukiliya da kanta bayan watanni da dama.

Shugaba Obama ya ce, ya kamata gamayyar kasa da kasa su yi bincike kan niyyar sabon shugaban kasar Iran Hassan Rohani wajen warware matsalar nukiliyar kasa ta hanyar diflomasiyya.

Ran 27 ga watan Satumba, shugaban Amurka Barack Obama ya tattauna tare da takwaransa na kasar Iran Hassan Rohani kan batun nukiliyar kasar Iran ta wayar tarho, abin da ya zama karo na farko da aka tattauna kai tsaye tsakanin shugabannin kasashen biyu cikin shekaru sama da 30.

Ran 24 ga watan Satumba, yayin da yake ba da jawabi a wajen babban taron MDD da aka yi a birnin New York, shugaba Rohani ya bayyana cewa, kasar Iran tana son yin shawarwari tare da kasashen da abin ya shafa, a sa'i daya kuma ya jaddada cewa, za a yi amfani da makamashin nukiliyar kasar kan harkokin kiyaye zaman lafiyar kasar ne kawai.

Bugu da kari, ran 18 ga watan Satumba, yayin zantawarsa na musamman da Gidan Rediyon kasar ta Amurka, shugaba Rohani ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Iran a karkashin jagorancinsa ba za ta raya makaman nukiliya ba, kuma yana da ikon kulla yarjejeniyoyin da abin ya shafa tare da kasashen yamma kan harkokin nukiliyar kasar Iran. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China