in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana fatan bangarori daban daban da batun Syria ya shafa za su sa kaimi ga gudanar da taron Geneva karo na biyu cikin hanzari
2013-11-06 20:22:23 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Laraba 6 ga wata cewa, Sin tana fatan bangarori daban daban da batun Syria ya shafa za su kara sa kaimi ga gudanar da taron Geneva karo na biyu cikin hanzari.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wakilin musamman mai kula da batun Syria Lakhdar Brahimi ya yi shawarwari tare da wakilan kasar Amurka da Rasha a birnin Geneva a ranar Talata 5 ga wata, inda ya bayyana cewa, bangarori daban daban da abin ya shafa ba su cimma daidaito kan lokacin gudanar da taron Geneva karo na biyu ba.

Hong Lei ya ce, hanyar siyasa ita ce hanya daya kawai wajen warware batun Syria, wadda kasa da kasa suka amince da ita. Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa wajen sa kaimi ga warware batun ta hanyar siyasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China