Hua Chunying ta ce, bisa kudurin da kwamitin gudanarwa na kungiyar hana amfani da makamai masu guba wato OPCW ya tsaida, babban direktan kungiyar ya gabatar da rahoto ga kwamitin gudanarwa karo na 34, inda aka bayyana kokarin da gwamnatin kasar Syria ta yi wajen aiwatar da kudurin da kuma halin gudanar da ayyukan binciken makaman da sashen sakatariyar kungiyar ya yi a kasar. Madam Hua ta ce, kasar Sin ta gamsu da halin aiwatar da kudurin a yanzu, kana ta yaba ma bangarori daban daban bisa ga kokarin da suka yi na aiwatar da ayyukan.
Ban da wannan kuma, Hua Chunying ta bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na kungiyar OPCW zai yi bincike kan rahoton babban direktan kungiyar da kuma tattauna shirin lalata makamai masu guba na nan gaba. Ta ce kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su ci gaba da yin kokari da kuma tsara shiri mai dacewa cikin hanzari. (Zainab)