Bisa labarin da aka samu daga Gidan Talabijin kasar na Syria, an ce, wasu boma-bomai sun fashe yayin da wasu 'yan ta'adda suka dana cikin wata mota a garin Yabrud da ke karkarar birnin Damascus. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10, yayin da mutane da dama suka jikkata,. Bugu da kari, fashewar ta lalata wasu shaguna da gidaje dake kusa da wurin.
Bisa labarin da aka samu daga kamfanin dillacin labaran kasar ta Syria ta SANA, an ce, a wannan rana, sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ga kungiyoyin 'yan ta'adda da ke birnin Damascus da kuma karkararsa, inda aka halaka 'yan ta'adda da dama.(Maryam Yang)