A wannan rana, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa, ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Iran Hasan Rouhani kan batun nukiliyar kasar Iran, inda ya nuna fatan kyautatuwar mawuyacin halin da kasashen biyu suke ciki, karkashin shawarwari karo na farko da aka aiwatar tsakanin shugabannin kasashen biyu cikin shekaru 30 da suka gabata.
Shugaba Obama ya bayyana cewa, yayin shawarwarin, ya sake jadadda matsayinsa da ya bayyana yayin babban taron MDD, watau ya yi imani cewa, za a warware matsalar nukiliyar kasar Iran daga dukkan fannoni. Bugu da kari, ya ce, idan kasar Iran za ta iya gaskata aniyarta wajen hana raya makamashin nukiliya ta hanyar dauka matakan da suka wajaba, hakan zai taimako sosai wajen kawar da takunkumin tattalin arzikin da gamayyar kasa da kasa suka kakabawa kasar Iran.
Mr. Obama ya kuma nuna cewa, idan za a iya warware batun nukiliyar kasar Iran, hakan zai ba da taimako wajen warware mawuyacin halin diplomasiyyar da ke tsakanin kasar Amurka da ta Iran cikin shekaru 30 da suka wuce, da kuma inganta zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.