A cikin gaba dayan wannan jawabi da aka watsa ta gidan talabijin na kasa ORTM, shugaba Ibrahim ya nuna rashin jin dadinsa kan abun kunyar da ya faru a ranar Litinin a Kati inda tsoffin sojojin da suka yi juyin mulki a karkashin janar Amadou Haya Sanogo suka yi bore domin neman a kara musu galar girma. Wannan hali na rashin da'a da barna ba za'a rufe ido kansa ba in ju shugaba Ibrahim da ya bukaci shugabannin sojojin kasar da su gudanar da bincike domin gano dalilai da masu hannu kan wannan abun kunya da ya abku a Kati.
Game da abin da ya faru Kidal inda 'yan tawayen Abzinawa na kungiyar MNLA da sojojin kasar Mali suka yi musanyar wuta a makon da ya gabata, shugaban kasar Mali ya bayyana cewa wata barazana ba za ta ci ba tare da daukar niyyar ganin zaman doka da oda sun tabbata a Kidal, Gao, Tombouctou da Koulikoro bisa 'yancin fadin kasar Mali baki daya. (Maman Ada)