in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na son ganin an fara taro kan batun Syria cikin sauri
2013-10-18 20:04:57 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta bayyana a ranar 18 ga wata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, cewa, kasar na son yin kokari tare da sauran bangarori masu ruwa da tsaki don ganin an fara taro na biyu a birnin Geneva kan batun Syria cikin sauri.

A cewar madam Hua, kasar Sin a tsaye take a kan ra'ayinta na cewa, matakan siyasa a maimakon na soja su ne hanyar mafita daya kadai ga matsalar da ake fuskanta a kasar Syria. Don haka, a wannan lokacin da ake kokarin gudanar da ayyukan gano makamai masu guba da lalata su a Syria, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara ba da taimako ga matakan siyasa, ba kawai tallafawa matakan kawar da makamai masu guba da MDD da kungiyar hana yaduwar makaman suke aiwatarwa ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China