in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da jerin sunayen kwararru 10 ga hukumar OPCW don shiga aikin bincike kan lalata makamai masu guba a kasar Syria
2013-10-08 20:10:24 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a gun taron manema labaru a yau Talata 8 ga wata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi maraba da ci gaba da aka samu kan batun makamai masu guba na kasar Syria, kana ta gabatar da jerin sunayen kwararru 10 ga hukumar hana amfani da makamai masu guba wato OPCW da za su gudanar da aikin bincike kan lalata makamai masu guba a kasar Syria bisa bukatun hukumar OPCW.

Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin na nuna goyon baya ga kudurin da kwamitin gudanarwa na hukumar OPCW da kwamitin sulhu na MDD suka tsaida, kuma tana fatan za a aiwatar da kudurin yadda ya kamata, kana tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su ba da taimako wajen aiwatar da kudurin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China