A cikin wata sanarwar da wani jami'in hukumar ta WFP dake kasar ta Kenya Ronald Sibanda ya fitar, an ce, za a dauki wannan mataki ne na rage yawan abincin da za a samar, da kaso 20 cikin 100 a watan Nuwamba da Disamba, domin tabbatar da abincin da aka samar ya kai karshen shekarar nan ta bana.
Hukumar WFP ta kimanta cewa, rage abinci da yawansa ya kai kashi 20 cikin 100, yana nufin 'yan gudun hijira ba za su iya samun isasshen abinci kamar yadda hukumar WHO ta tsara ba. Don haka Sibanda ya yi kira da jama'a, da su ba da taimako ga 'yan gudun hijirar, don biyan bukatunsu wajen samar da isasshen abinci.(Bako)