A daren ranar Alhamis 17 ga wata ne dai, gidan rediyon BBC ya gabatar da wani shiri da ya nuna cewa, 'yan sandan Norway na kokarin binciken alakar dake tsakanin wani dan kasar da ake kira da Hassan Abdi Dhuhulou da harin da aka kaddamar a kasar ta Kenya. Hassan Abdi Dhuhulou, dan shekaru 23 a duniya, dan asalin kasar Samali ne. Kuma a shekarar 1999, iyalansa suka yi kaura zuwa Norway a matsayin 'yan gudun hijira. Ana dai tuhumar wannan saurayi da hannu cikin tsarawa, da kuma kai hari a wannan babban kanti dake Nairobi, babban birnin kasar ta Kenya. A kalla, wannan hari na tsawon kwanaki hudu ya haddasa mutuwar mutane 67, yayin da koma aka rasa inda wasu da harin ya ritsa da su suka shiga.
Hukumar leken asiri ta Norway ta ce, an riga an tura jami'ai zuwa Kenya domin yin bincike kan labarin da aka bayar dangane da hakan. Amma har yanzu gwamnatin Norway ba ta tabbatar da sunan wanda ake tuhumar ba.
Kawo yanzu dai babu wata masaniya kan hakikanin yawan maharan da suka kaddamar da wannan hari.
Da farko, 'yan sanda sun kiyasta cewa, maharan 10 zuwa 15 ne suka kai harin, amma bisa bidiyon da mahukuntan Kenya suka fitar a baya bayan nan, an ga mutane hudu kawai. Wani dan majalisar dokokin kasar ta Kenya ya ce, watakila gawawwaki biyu da aka samu bayan aukuwar lamarin, na wasu daga cikin dakarun ne.
Kafin hakan dai tuni, kungiyar al-Shabab dake da alaka da al-Qaeda ta yi shelar daukar alhakin wannan hari.(Fatima)