Jami'ar ta kuma bukaci Amurka da ta inganta tsarin amincewa juna wajen kiyaye dokoki, domin kaucewa tasirin da leken asiri ka iya yi ga shawarwarin da suka jibanci daddale yarjejeniyar kafa dangantakar abokantaka ta saka jari, da yin cinikayya a ketaren tekun Atlantic.
Reding ta ce, kwanan baya, sa-in-sa game da satar bayanai da ke tsakanin kasar Amurka da kasashen Turai, ya lahanta dangantakar sada zumunta tsakanin bangarorin biyu, kuma bai kamata kawancen kasashen biyu su rika satar bayanin juna ba, duba da cewa satar bayanai ba zai kawo aminci ga kasashen ba, don haka ya dace Amurka ta dauki hakikanin matakai don inganta amincewa juna.
A wata sabuwa kuma, a wannan rana, yayin da wata tawagar kwamitin kula da dangantakar kasashen waje ta majalisun dokokin kasashen Turai ke zantawa da mataimakin sakatare harkokin waje dake kula da batun siyasa, na majalisar gudanarwar Amurka Wendy Sherman, ta nemi karin bayani daga Amurkan.
Sai dai, a ranar 29 ga wata, yayin da shugaban hukumar tsaron kasar Amurka Keith Alexander, ke ba da shaida a majalisar dokokin kasar, ya ce, kwanan baya, kafofin yada labaru na kasashen Turai sun bayyana cewa, hukumar leken asirin Amurka ta saci bayanai daga wayoyin salula na jama'ar kasashen kungiyar EU, wannan bayani a cewar sa babban kuskure ne.
Ya ce, irin wadannan bayanai da Amurka ta samu, ba wai Amurka ta same su daga gefe guda kurum ba, amma aikin leken asiri ne da Amurka da kawacen abokanta na kungiyar tsaro ta NATO suka yi tare don tabbatar da tsaro. Haka kuma, ya musunta zargin sa ido ga al'ummar kasashen Turai da Amurka ta yi, amma bai bayar da karin bayani game da batun ba.(Bako)