Tsohon babban edita na jaridar Washington, shehun malamin jami'ar jihar Arizona na yanzu, Mr. Leonard Downie ya rubuta wannan rahoto, inda ya bayyana cewa, yawan karar da suka shafi bayyana asirin gwamnati da kuma takardun bincike da 'yan jaridu suka bankado da gwamnatin Barack Obama ta sata ya fi ko wace gwamnati yawa. Kuma rahoton ya ruwaito maganganun shahararrun 'yan jaridu da kuma labarai da dama cewa, gwamnatin Barack Obama na mai da hankali sosai dangane da ikonta kan 'yan jaridu, har ta samar da matakai masu tsanani bayan gwamnatin Richard Milhous Nixon don sa ido kan labaran da ake watsawa.
Bisa rahoton Downie da sauran labaran da aka bayar, an ce, akwai hanyoyi hudu da gwamnatin kasar Amurka ta sa hannu cikin harkokin kafofon watsa labaru na kasar, na farko shi ne daukar matakan sa ido kan kafofin watsa labaru da 'yan jarida. Na biyu shi ne kai hari ga masu gabatar da labaran dake shafar gwamnatin. Na uku kuwa shi ne tsoma baki kan ayyukan kafofin watsa labaru da sunan "moriyar kasa" ko "asirin aikin soja". Kuma na hudu shi ne gabatar da labarai marasa gaskiya don ta sarrafa kafofin watsa labaru kai tsaye kamar yadda take bukata.
Bayan da wani dan jarida daga kasar waje ya duba tsarin zamantakewar al'ummar kasar Amurka a shekaru da dama da suka gabata, ya nuna cewa, gabatar da labarai a kasar Amurka shi ne fadakar da abubuwan da gwamnatin kasar take so. Kana wani mashahurin masani na kasar Amurka Avram Noam Chomsky ya rubuta wani bayani, inda ya nuna cewa, yadda ake sarrafa tunani Amurkawa ya wuce tsammani. Abin da aka bayyana a cikin rahoton Downie shi ne sa ido da gwamnatin kasar Amurka ta yiwa kafofin watsa labaru, kana ta yi wannan aiki a cikin sirri har yanzu da ya fito fili, kamar yadda aka bayyana a cikin wani bayanin da aka gabatar a mujallar "National Interest" ta kasar Amurka cewa, gwamnatin Amurka ta tsoma hannu ba kayyadewa. (Maryam+Zainab)