Ranar ta zo daidai da ranar cikon shekaru 12 da daddale dokar magance ta'addaci ta kasar Amurka. A wannan rana, kungoyoyi da kamfanoni fiye da dari daya na kasar sun yi zanga-zanga a wurin dake dab da babban ginin majalisar dokokin kasar dake birnin Washington don nuna adawa ga ayyukan sa ido da hukumar kiyaye tsaron kasar da sauran hukumomin leken asiri na kasar suka yi. Da karfe 2 na yammacin ranar, mutane kimanin dubu daya sun shiga zanga-zangar a muhimman wuraren kasar, rike da allunan da ake rubuta kalmomin "dakatar da ayyukan sa ido", "dakatar da sa ido gare mu", har ma "nuna godiya ga Edward Snowden" da dai sauransu.
Shugaban reshen kungiyar kawancen samun 'yancin jama'ar kasar Amurka ya bayyana a wurin yin zanga-zangar cewa, bayan abkuwar harin ta'addanci da aka kai a ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 2001, gwamnatin kasar Amurka ta gudanar da ayyukan sa ido ga jama'a sosai, hukumomin leken asiri sun samu babban iko na wuce gona da iri. (Zainab)