in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kudi na Amurka ya yi kira ga jam'iyyu biyu na kasar da su kawar da sabani don magance samun koma bayan tattalin arziki
2013-10-22 10:42:33 cri
A ranar 21 ga wata,wani babban jami'in hukumar kula da ajiyar kudaden kasashen waje ta kasar Amurka Charles Evans ya ce, hukumar na bukatar rahotonnin da za su iya shaida kyautatuwar halin da ake ciki na samun guraben aikin yi don tabbatar da samun karuwar tattalin arziki yadda ya kamata, kuma ana bukatar watanni da dama don tantance halin da ake ciki, wato ke nan hukumar ba za ta dauki matakai ba a watan Oktoba.

Don haka in ji shi hukumar kula da ajiyar kudaden kasashen waje ta Amurka tana fatan ganin cewa, za a kara samar da guraben aikin yi da yawansu zai kai dubu 200 cikin kowane wata, kuma yawan mutanen da suka rasa guraben aikin yi zai ci gaba da raguwa.

Mr. Evans a sa'i daya kuma ya yi bayanin cewa yadda aka rufe wasu sassan gwamnatin Amurka cikin makwanni da dama da suka gabata, ya kawo rashin tabbas game da makomar tattalin arzikin kasar, sabo da yarjejeniyar da aka daddale a tsakanin jam'iyyu biyu cikin ganganin lokaci, zai kawo matsala a farkon shekara mai zuwa, da kyar za a tabbatar da cewa, ba za a sake fuskantar halin kunci game da tattalin arziki ba, sabo da haka, da wuya a yanke shawara game da daidaita manufar sakin bakin aljihu.

A ranar 21 ga wata, ministan kudi na kasar Amurka Jacob Lew ya ce, ya kamata jam'iyyu biyu a majalisar dokokin kasar su kawar da sabanin da ke tsakaninsu, don kaucewa lahanin da sabanin zai iya kawo wa tattalin arzikin kasar. A wannan rana kuma, Lew ya yi bayani a jaridar New York Times cewa, tattalin arzikin Amurka bai samu saurin bunkasa ba, kuma ana bukatar kara saurin samar da guraben aikin yi, haka kuma ganin yadda gwamnati ke fama da matsalar harkar kudi a kwanakin nan, wato ke nan, rikicin siyasa yana ta kawo cikas game da gaggauta raya tattalin arzikin kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China