in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Jamus, Faransa da Italy sun kushe gwamnatin Amurka
2013-10-24 15:22:41 cri
Kwanan baya, kasashe da dama sun kushe gwamnatin Amurka bisa laifin da ake zargen ta na satar bayanai daga wayoyi na kasashensu.

Kasar Jamus ta kasance wata muhimmiyar kasa da take kukan wannan matsalar. A ranar 23 ga wata, kakakin gwamnatin Jamus Steffen Seibert ya ba da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, gwamnatin Jamus ta samu bayanin cewa, watakila hukumar liken asiri ta CIA ta Amurka tana satar bayanan shiga da kuma fita daga wayar salula ta firaministar kasar Jamus Angela Merkel. Game da wannan, Jamus ta riga ta tambayi kasar Amurka, kuma tana bukatar Amurka da ta yi karin bayani game da batun.

A cikin sanarwar, an ce, a wannan rana, Angela Merkel ta buga waya ga shugaban kasar Amurka Barack Obama, inda ta bayyana cewa, tana adawa ga irin aika-aika na satar bayanai, kuma ba za ta amince da wannan ba. A sa'i daya kuma, tana fatan Amurka za ta yi karin bayani game da batun.

A gun taron manema labaru da aka saba yi a wannan rana, kakakin fadar White House ta Amurka Jay Carney ya bayyana cewa, shugaban Obama ya ba da tabbaci ga Angela Merkel cewa, Amurka ba ta aikata hakan yanzu, kuma ba za ta saci bayanai daga firaministar ba, kuma ya amince da inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin liken asiri na kasashen biyu. Amma, Obama bai tabo maganar ko hukumar CIA ta taba satar bayanai daga wayar Madam Merkel a baya ba.

Wannan ba shi ne karo na farko da shugaba Obama ya fuskanci wannan tambaya ta waya ba. Tuni, gwamantin Faransa ta yi Allah wadai da satar bayanai da Amurka ta yi da kakkausan harshe, haka kuma, shugaban kasar Faransa François Hollande shi ma ya nuna rashin jin dadi game da batun ga Obama ta waya.

A wata sabuwa kuma, kasashen Italy da Mexico, su ma suna jira karin bayanai daga kasar Amurka game da batun.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China