Mr. Steine ya ce, kasar Sin na mai da hankali sosai kan kiyaye muhallin halittu, ta kuma sa kaimi ga kamfanoni masu zaman kansu da su ci gaba da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli yayin da suke gudanar da ayyukansu. Matakan da kasar Sin ta dauka sun nuna kokarinta wajen neman daidaito tsakanin bunkasa tattalin arziki da kuma kiyaye muhalli, sannan kuma za ta ci gaba da haka a nan gaba. Lamarin ya zama wata babbar dama ga kasashe masu neman daidaito tsakanin kiyaye muhalli da neman bunkasuwa. (Maryam)