Kwanan baya, ma'aikatar kula da zirga-zirga da sufuri ta kasar Sin ta buga takardar ba da shawara wajen gaggauta ga kafa tsarin yin zirga-zirga da sufuri ba tare da gurbata muhalli ba, inda aka sa niyyar kafa irin wannan tsari kafin shekarar 2020.
An ba da labari cewa, wannan ne karo na farko da Sin ta gabatar da irin wannan shawara, wanda ya shafi jiragen kasa, hanyoyin mota, jiragen ruwa, jiragen saman fasinja, da wasiku da sauransu. Abin da ya kasance wani babban tsari gaba daya a dukkan kasar wajen yin zirga-zirga da sufuri ba tare da gurbata muhalli ba.
Wannan takardar ta gabatar da ayyuka 22 dake shafi fannoni biyar domin cimma burin yin zirga-zirga da sufuri ba tare da gurbata muhalli ba, wadanda suke kunshe da wasu abubuwa ciki hadda yin tsimin albarkatun kasa, yin amfani da makamashi, kayyade fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da kiyaye muhalli da sauransu. Takardar ta nemi bunkasa sha'anin zirga-zirga da sufuri tare da yin la'akari da kiyaye muhalli. (Amina)