Cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta zuba darurruwan biliyoyin yuan kan manyan ayyukan kare dabbobi da tsire-tsiren, gina yankunan kiyaye muhallin halittu da kuma kiyaye dazuzzuka da dai sauran harkoki, ta yadda za a kyautata yanayin kiyaye dabbobin daji wadanda ke kusan karewa a nan duniya. Amma har zuwa yanzu, akwai dabbobin daji da dama dake dab da kusan karewa a kasar Sin. (Maryam)