in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a kara sa lura kan kasashen Afirka yayin da ake tsara shirin samun bunkasuwa bayan shekarar 2015
2013-10-26 17:26:46 cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a ranar 25 ga wata cewa, kamata ya yi kasashen duniya su sa lura kan kalubale da bukatun bunkasuwar kasashen Afirka, da matsalolin da suke fustanka yayin da ake tsara shirin samun bunkasuwa bayan shekarar 2015, domin kawar da talauci da sa kaimi ga samun bunkasuwa a dukkan fannoni a nahiyar.

Yayin gudanar cikakken zama na babban taron MDD karo na 68 a wannan rana, an tattauna batun aiwatar da sabon shirin raya kasashen Afirka, da dalilin da ya sa aka samu rikice-rikice a nahiyar da kuma matakan da za a dauka don samun zaman lafiya da bunkasuwa. A gun taron, Wang Min ya bayyana cewa, kamata ya yi a kara sa lura kan nahiyar Afirka a cikin shirin samun bunkasuwa bayan shekarar 2015. Kana ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su cika alkawarin da suka yiwa kasashen Afirka, da girmama ikon kasashen, da kuma nuna goyon baya gare su a kokarinsu na samun zaman lafiya da karko.

Game da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, Wang Min ya bayyana cewa, bayan kulla sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka, an zurfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da ma kungiyar AU. Kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen raya yankinsu bisa tsarin bai daya, tare da kara taimakawa wajen aiwatar da sabon shirin raya kasashen na Afirka. Ban da wannan kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a nahiyar Afirka a watan Maris na bana, inda ya sanar da wasu sabbin matakan Sin na nuna goyon baya ga bunkasuwar nahiyar Afirka. Kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasashen Afirka wajen ci gaba da zurfafa hadin gwiwa, da kuma inganta dangantakarsu don samun moriyar juna da cimma buri tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China