A cikin bayaninsa mai taken 'Sabuwar Hanyar Siliki da ta bi ta nahiyar Afirka', Kevin Taylor ya ce, alkaluman sun sheda cewa, a shekaru 10 da suka wuce, tattalin arzikin nahiyar Afirka yana karuwa cikin sauri. Cikin kasashe da yankuna 10 mafi samun saurin tasowar tattalin arziki, ana samun kasashe 6 daga nahiyar Afirka. Sa'an nan, cikin wadannan shekaru, yawan cinikayyar dake tsakanin Sin da Afirka ya karu daga dala biliyan 11 zuwa biliyan 166. Yanzu kasar Sin ta riga ta zama kasar da ta fi kowace kasa a duniya zuba jari a nahiyar Afirka.
Kevin Taylor ya kara da cewa, cinikayyar dake gudana tsakanin kasashen Asiya da na Afirka za ta dinga kara kasonta cikin cinikin kasa da kasa, kana yankin gabas ta tsakiya, a matsayin yankin da ya hada nahiyoyin 2, zai taka muhimmiyar rawa musamman ma a fannin sufuri da jigilar kaya. Ta haka, inji bayanin Taylor, sannu a hankali, za a samu wata 'sabuwar hanyar siliki', da ta shafi kasashe da yawa dake nahiyoyin Asiya da Afirka, da wata al'ummar da yawanta ya kai biliyan 5.5.(Bello Wang)