Game da bayanin da wasu kafofin yada labaru suka gabatar a kwanan baya cewa, wai akwai wasu matsaloli game da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, a ranar Jumma'a 14 ga wata, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Sin, madam Hua Chunying ta mai da martani a nan birnin Beijing cewa, tun asali an kafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu ba ta fatar baka ba kawai, bisa kokarinsu ne duka. Gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka, kuma za ta ci gaba da daidaita matsalolin da za a iya fuskanta a yayin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka cikin tsanake.
Hua ta ce, bisa kokarin bangarorin biyu, dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka na bunkasa cikin sauri a yanzu, kuma tana kan sabon matsayi a tarihi. An kafa wannan dangantaka ne ba ta fatar baka ba kawai, a maimakon haka, bangarorin biyu suna sada zumunci da girmamawa juna da moriyar juna cikin adalci, tare da neman samun bunkasuwa tare.(Fatima)