in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Michel Platini Na Son Sauya Matsayin Gasar UEFA
2013-11-29 16:03:07 cri

Ban da haka Blatter ya yi kokarin yada gasar zuwa Afirka da Amurka ta Kudu. Ga misali gasar shekarar 2010 ta samu gudana a kasar Afirka ta Kudu, yayin da gasar shekarar 2014 za a yi ta a kasar Brazil. Wadannan matakan sun shaida yadda mista Blatter yake kokarin rungumar nahiyoyin Asiya, da Afirka, da Amurka ta Kudu, gami da neman dakile tasirin nahiyar Turai a fannin wasan kwallon kafa.

Da farko dai mun san cewa nahiyar Turai na ci gaba da zama wani yanki mai matukar muhimmanci a fannin wasan kwallon kafa, ganin yadda Premier League, da La Liga, da Serie A, da Bundesliga suka kasance manyan gasanni mafi karbuwa ga 'yan kallo, wadanda kuma ake gudanar da su a wannan nahiya. Kana kuloflikan kasashen Turai suka kasance mafiya karfi a duk fadin duniya. Sai dai a fannin kungiyoyin kasashe, kungiyoyin Turai ba su da wani fifiko sosai, idan an kwatanta da kasashen Brazil da Argentina, da Japan, da kuma kasashe da dama dake nahiyar Afirka.

Ana ganin hakan ne ya sa Platini ke neman tallafawa kungiyar Spain don ta samu damar lashe gasar cin kofin duniya, ganin yadda kungiyar take da karfi sosai a halin yanzu, take kuma kunshe da fitattun 'yan wasa na kuloflikan Bacelona da Real Madrid. Ban da haka, ya yi kokarin habaka tsarin gasar cin kofin nahiyar Turai, don kar hukumar FIFA ta hadiye ribar da manyan gasannin kasa da kasa suke samarwa duka.

An ce gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010, ta samar da ribar da ta kai dalar Amurka biliyan 4.9, inda kashi 75% na kudin aka mika ma hukumar FIFA, wato kimanin dala biliyan 3.7 ke nan. A nata bangaren, gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekarar 2012 ta samar da ribar da ta kai dala miliyan 1827, kudin da a cikin sa aka ware ma hukumar UEFA dala miliyan 270. Idan mu kwatanta wannan kudi da dala biliyan 3.7 da FIFA ta samu, za mu ga yadda ribar da UEFA ta samar ta yi kadan matuka. Amma burin da Platini ke neman cimmawa shi ne, samo karin riba daga hannun hukumar FIFA, ganin idan tsarin gasar UEFA ya habaka, zai kara janyo zuba jari a tsarin gasar cin kofin nahiyar Turai.

Ban da kokarin habaka tsarin gasar, Platini yana neman tallafawa kungiyoyi marasa karfi dake nahiyar Turai, domin ba ya son ganin wasu kasashen kamarsu Birtaniya, da Spain da dai sauransu sun samu makudan kudin raya harkar wasan kwallon kafa, yayin da wasu sauran kasashe ke ci gaba da kasancewa a can baya.

Daya daga cikin irin wannan tallafin shi ne sanya karin kungiyoyi halartar gasar cin kofin nahiyar Turai, ta yadda wasu kananan kuloflika su ma za su iya samun damar nuna kwarewarsu, kana bisa damar halartar gasar za su samu kudaden shiga masu yawa, matakin da zai ba su zarafin gamsuwa, da kara yaba ma Michel Platini, shugaban hukumar wasan kwallon kafar nahiyar Turai. (Bello Wang)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China